Wannan nuna goyon baya ga dan takarar jam’iyar APC kuma shugaban kasa Muhammadu Buhari da kungiyar Izala ta yi cewa shine dan takarar da za a zaba a zaben dake tafe, tuni ya soma samun martini daga wani bangare na kungiyar da kuma masana.
Tun farko dai shugaban kungiyar Izala bangaren Kaduna Sheikh Abdullahi Bala Lau, a zantawarsa da manema labarai a Yola jim kadan bayan kammala wani taro da suka yi,,ya bada fatawar a zabi shugaba Buhari. To sai dai kuma da alamun yanzu haka wannan fatawa ta su Bala Lau, ta janyo cece-kuce inda daya bangaren Izala a Najeriya wato bangaren Jos, suka ce bada yawunsu ba.
Sheikh Nasir Abdulmuhyi,yace duk da cewa suna goyon bayan shugaba nagari, toh amma su basu kai ga daukan mataki ba. Abdulmuhyin wanda ya bayyana dalilan da suka sa bangaren su Bala Lau,ke nuna goyon baya a yanzu, yace bai kamata ake yi musu dibar karan mahaukaciya ba.
Duk da cewa Najeriya kasa ce ta yar ba ruwanta da addini, amma ko a zaben shekarar 2015, wasu kungiyoyin addini a kasar sun nuna irin wannan goyon baya, batun da masana irin su Barr. Sunday Joshua Wigra ke ganin akwai abun dubawa.
Ga cikakken rahoto da Ibrahim Abdulaziz ya aiko mana:
Your browser doesn’t support HTML5