Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Lamarin Tsaro Ya Sa MDD Ta Kwashe Wasu Ma’aikatan Agajinta Daga Najeriya


ADAMAWA: 'Yan gudun hijira da za'a rufe sansaninsu
ADAMAWA: 'Yan gudun hijira da za'a rufe sansaninsu

Majalisar Dinkin Duniya ta janye ma'aikatanta na agaji 260 a bisa dalilin ta'azara da yanayin tsaro ya yi a arewa maso gabashin Najeriya.

Wakilin MDD mai sa ido a ayyukan agaji a Najeriya, Mista Edward Kallon, shine ya bayyana hakan a wata takarda ta musamman da ya aikewa manema labarai.

A cikin takardar ya ce daga 26 ga watan Disambar bara Mutane sama da dubu 30 ne suka bar muhallan su zuwa wasu garuruwa a cikin Najeriya.

Mista Edward ya ce babban abin takaicin shine yadda mata da yara, sune suka fi galabaita a wanan yanayi, domin suna share kwana da kwanaki suna tafiya a kafa a halin kunci da yunwa da kishir ruwa da kuma tsoro abin da ka iya biyo baya.

Ganin cewa Abuja tana cikin garuruwan da ke da yan gudun hijra da dama tun lokacin da kasar ta shiga halin ta'addancin ‘yan Boko Haram, hakan ya sa Muryar Amurka ta tuntubi Shugaban Hukumar bada agajin gaggawa ta birnin tarayya Alhaji Garba Abbas, wanda ya tabbatar da cewa an sami karin ‘yan gudun hijira daga jihohin Borno da Adamawa wanda ya kawao jimla dubu 20 kuma an samu karuwar wasu dubu 10 daga Jihohin Kogi da Nasarawa wadanda fadace-fadacen cikin gida ya shafe su.

Alhaji Garba, ya ce ministan ma'aikatar birnin tarayya ya bada umurnin taimakawa ‘yan gudun hijran wajen kula da lafiyarsu da abincin su. Doka ta hana a gina sansononi amma an yi masu matsuguni inda suke samun kula sosai.

Amma dan Majalisar Wakilai mai kula da kwamitin sa ido a tallafin da gwamnatin tarayya Najeriya ke bayarwa Alhaji Sani Zoro, ya ce Kamata yayi Gwamnatin ta rika tanadin abubuwan da yan gudun hijran ke bukata a duk lokacin da aka kai hari a garuruwan su saboda dole ne wadansu za su gudu domin neman tsira.

Wanan mataki na janye ma'akatan jinya da Majalisar Dinkin Duniya ta yi yana iya haifar da wagegen gibi a kokarin da hukumomi ke yi na magance matsalolin da ‘yan gudun hijran ke fuskanta.

Domin karin bayani saurari rahotan Medina Dauda.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:15 0:00

Facebook Forum

Zaben 2023

TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Tasirin Da Zaben Donald Trump Zai Yi A Harkokin Kasashen Duniya.
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:50 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG