Masu iya magana na cewa ra'ayi riga, kowa da irin tasa, ‘yan Najeriyar dai na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu dangane da allurar riga-kafin cutar Covid-19 da aka fara yi wa mutane a Najeriya.
Ranar Asabar ne shugaba Buhari da Mataimakinsa Osinbajo suka sami riga-kafin wanda aka nuna kai-tsaye a talbijin, kwana guda bayan fara shirin riga-kafin COVID-19 na kasa.
Duk da yake shugaban ya yi hakan ne domin tabbatarwa da ‘yan Najeriya ingancin riga-kafin, tare da janyo hankulan ‘yan kasar da su tabbatar sun ba da hadin kai don ganin an kawo karshen wannan annoba.
Amma da yawa daga cikin mutane na bayyana ra’ayin cewa ba allurar riga-kafin coronavirus ce a gaban ‘yan Najeriya, cutar da ta fi kashe mutane ita matsalar tsaro a kasa.
Sai dai ba duk mutanen da aka ji ra’ayoyinsu ba ne, suke sukar allurar, wasu da yawa sun yaba da samar da wannan riga-kafin cikin sauri tare da taimakawa kasashe matalauta.
Saurari ra’ayoyin ‘yan Najeriya game da riga-kafin a wannan rahotan na Shamsiyya Hamza Ibrahim.
Your browser doesn’t support HTML5