Shugaba Buhari da Mataimakinsa Osinbajo sun sami riga-kafin wanda aka nun kai-tsaye a talbijin, kwana guda bayan fara shirin riga-kafin COVID-19 na kasa da aka fara yi wa ma’aikatan kiwon lafiya da ma’aikatan babban Asibitin Kasa da ke Abuja.
Bayan da aka masa allurarsa ta farko, shugaba Buhari ya ce “Na karbi allurata ta farko kuma ina so na yaba wa duk ‘yan Najeriya da suka cancanta, su yi hakan domin a kare mu daga kwayar cutar,” kamar yadda wata sanarwa daga fadar ta bayyana.
Karin bayani akan: AstraZeneca, COVID-19, Coronavirus, Buhari, Nigeria, da Najeriya.
Shugaba Buhari ya bukaci dukkan gwamnatocin jihohi da shugabannin gargajiya da kuma shugabannin addinai, da su kasance masu jagoranci a kokarin hada kan yankunansu domin wayar da kan al’umma.
Ya kuma ba da tabbacin cewa alluran AstraZeneca wadda Najeriya ta samu, za su rika zuwa ne rukuni-rukuni farawa da alluran miliyan hudu da aka riga aka karba.
Haka kuma shugaban ya ce tsarin karba da yi wa ‘yan Najeriya alluran daga wannan shekarar ta 2021 zuwa 2022, zai tabbatar da an yi wa sama da kashi 70 na mutanen Najeriya.
A farkon makon nan Najeriya ta fara karbar rukunin alluranta karkashin shirin COVAX da ke tabbatar da raba daidai ga kasashen duniya da zimmar ganin ba a bar kasashe masu tasowa a baya ba.