A shekara 2020 ne Amurka ta ayyana Najeriya a matsayin kasa da ke tauye yancin mabiya addinai daban daban da ake da su a kasar, amma da wannan jawabin na Anthony Blinken, yanzu Najeriya ta fice daga cikin jerin kasashen da aka hada a wannan shekara ta 2021.
Shugaban gudanarwa ta Kungiyar Amnesty International Auwal Musa Rafsanjani yana ganin wannan mataki da Amurka ta dauka ya yi daidai domin tun dama ba mutane da dama ba su goyi bayan cewa Najeriya kasa ce da ke tauye ýancin addini ba domin kowa da ke kasar yana irin bautar da yake so ne.
Rafsanjani ya ce gwamnati bata taba sa baki a yadda mutanen kasar ke addinin su ba, sai dai wasu 'yan kasa ne kawai suka zuga Amurka a lokacin da ta sa Najeriya a ayarin masu tauye 'yancin addini.
Shi kuwa Malamin Tsangayar siyasa da diflomasiyar kasa da kasa a Jamiár Abuja Dokta Bibi Farouk yana ganin za a iya kalon wannan mataki da kasar Amurka ta dauka ta fanoni uku, kuma wanda yake da inganci shi ne cewa Najeriya tayi aiki sosai ta fanin diflomasiya, kuma ta nuna cewa irin wannan batu abune da ake yi a bayan fage ba a bayyane ba. Bibi ya ce abu na biyu shine cewa an yi bincike an gano kowa yana addinin da ya so ne a Najeriya, babu wanda yake tsangwaman wani saboda addinin sa. Abu na uku kuma ,tsarin tafiyar da diflomasiya a kasa, akwai yarda cewa abubuwa da ke faruwa a cikin gida suna da tasiri akan yadda kasar take tafiyar da harkokin ta na waje.
sababbin-kudurorin-amurka-kan-nahiyar-afirka
ziyarar-sakataren-gwamnatin-amurka-anthony-blinken-a-najeriya
gwamnatin-najeriya-na-dakon-rahoton-gwamnoni-kafin-ta-dauki-mataki-kan-batun-endsars
Amma ga babban mukarabbin mallam ibrahim Elzakzaki na kungiyar shiá Mohammed Ibrahim Gamawa yana ganin ba a yi wa yan Shiá adalci ba, saboda Amurka tana gani aka yi wa ýaýan kungiyar kisan mumuke amma yanzu sai ta fito ta ce ta wanke Najeriya da sabulun salo? Gamawa ya ce akwai abin dubawa.
A ayarin kasashen da ke tauye yancin addini na shekara 2021 akwai kasashe 10 ciki har da kasar China da Rasha. Anthony Blinken ya ce gwamnatin Amurka za ta cigaba da saka takunkumi kan kasashe da gwamnatocin ke hana yan kasar yin addinin da suke so.
Saurari cikakken rahoton Madina Dauda cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5