Ra'ayoyin Wasu 'Yan Najeriya Akan Rasuwa Da Tarihin Da Muhammad Ali Ya Kafa

A yayin da ake ci gaba da makokin rasuwar zakaran dan damben duniyan nan na kasar Amurka da ya rasu ranar juma’ar da ta gabata Muhammad Ali, wakilin sashen Hausa na Muryar Amurka Murtala Farouk ya jiyo mana ra’ayoyin wasu akan irin yadda suka ji yayin da suka sami labarin rasuwar marigayin.

Malam Abba Lawan Kurmawa shine na farko da ya fara da cewa “Gaskiya abin da zan iya cewa anan akan maganar rasuwar Muhammada Ali shine tamkar ni aka yi wa wannan rashi domin kuwa ta dalilin shin a shiga harkar dambe, saboda yadda nake kallon yadda yake wasan sa, shi yasa lokacin da nake makaranta na jajirce wajan ganin shugaban makarantar mu ya bude mana fili domin yin damben boxing, kai harma na taba wakiltar jahar Kano, da tsohuwar gundumar Sumaila”.

Sai kuma malam Yahaya Mai Yaki wanda shi kuma ya ce “ Rasuwar shahararren dan damben duniya Muhammad Ali, rasuwa ce data girgiza duniya baki daya, domin kuwa duk wanda yasan tarihin sa yasan cewa mutum ne wanda yayi iya bakin kokarin sa domin daukaka wasan damben Boxing na duniya baki daya. Mutum ne wanda ya shahara kuma yayi suna kwarai”

Haka Aminu Abdullahi Abubakar da kuma Adamu Suleman wadanda suka bayyan nasu ra’ayin musamman ganin yadda Muhammad Ali yake bakar fata kuma musulmi dan kasar Amurka, wannan yasa jama’a da dama alfahari a cewar su, kamar yadda su yi farin ciki lokacin da shugaba Obama ya kasance bakar fata na farko da yayi nasarar lashe zaben kasar ta Amurka.

Ga cikakken rahoton.