Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yawan Shiga Rana Na Haifar Da Cuttutuka Da Dama Ga Lafiyar Mutun


Ya waita barin fatar jikin mutun a cikin rana, na nakasar da naman jikin mutun. A wani bincike da wasu masana suka gudanar, wanda Dr. Jason Reichenberg, na tsangayar kula da kwayoyin cuttutukan fata, a jami’ar Dell Texas-Austin, ya bayyanar da cewar, matukar mutun na ya waita shiga cikin rana, batare da samar da wasu sunadarai da suke taimakama fatar jiki ba, to hakan nada matukar illa.

Binciken su ya gano cewar, idan mutun ya yawaita barin fatar jikin shi na shan rana, to za’a kai wani mataki idan shekarun mutun sun kai wani lokaci, fatar ba zata iya kare tsokar jikin mutun ba. Daga nan wasu cuttutuka suna iya shiga cikin jikin mutun a sanadiyar fatar bata gudanar da aikin ta yadda ya kamata.

Sun kara da cewar, babban abu kawai da fatar jikin mutun take bukata shine, mutun ya dinga kokarin bama fatar damar shan rana na bitamin D, wanda take fitowa da safe kamin rana tayi zafi, wannan nada matukar muhimanci ga lafiya mutun. Haka idan mutun na samun isashen bacci, to babu bukatar sai mutun ya dinga wasu shafe-shafe don gyaran fata. Hasalima, wasu daga cikin kayan shafe shafe da mutane kan sa a jikin su, kan iya zama cuta ga fatar, amma ba dole ne mutun ya gani ba, alhali daga ciki fatar tana samun rauni.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG