Qatar: Saudiyya Ta Janye Dan Wasanta Saboda Samun Shi Da Laifin Amfani Da Kwaya Mai Kara Kuzari

Tawagar 'yan wasan Saudiyya

Hukumar da ke yaki da tu’ammali da kwayoyin masu saka kuzari  ta nemi a yanke masa hukuncin da ya fi wata 18.

An cire Fahad al-Mowallad, daya daga jerin ‘yan wasan kasar Saudiyya da za su wakilce ta a gasar cin kofin duniya da za a fara a Qatar.

Hukumar kwallon kafar kasar ta Saudiyya ta cire Al-Mowallad ne saboda akwai shari’a da ake yi a kansa, kan samun burbushin Furesemide, wata kwaya da ke boye kwayoyin da ke kara kuzari.

A watan Fabrairu aka samu burbushin kwayar a jikin Al-Mowallad, amma duk da haka an saka shi a jerin ‘yan wasan.

An yanke masa hukuncin haramcin buga kwallo na tsawon wata 18.

Sai dai daga baya an janye shi a wani abu da kasar ta kira mataki na “kandagarki.”

Hukumar da ke yaki da tu’ammali da kwayoyi masu saka kuzari ta nemi a yanke masa hukuncin da ya fi wata 18.

Saudiyya na rukunin C a gasar ta cin kofin duniya, inda za ta fafata da Argentina, Poland da Mexico.