Qadhafi Yana Zargin Al-Qaida Kan Boren Da Ake Yi A Libya

Shugaban Libya Moammar Gadhafi.

Mayakan sakai da sojojin haya daga ketare a Libya sun kai farmaki kan zobe da masu zanga zanga dake kyamar gwamnatin kasar suke yi wa babban birnin kasarTripoli

Mayakan sakai da sojojin haya daga ketare a Libya sun kai farmaki kan zobe da masu zanga zanga dake kyamar gwamnatin kasar suke yi wa babban birnin kasar Tripoli,a lokacinda shugaban kasar Moammar Gadhafi yake zargin ‘yan hamayya da cewa suna karkashin Osama Bin Laden.

An yi mummunar zubda jinni a jiya Alhamis a birnin Zawiya mai tasarar kilomita 50 daga babban binrin kasar.’Yan kasar Libya da suka gudu daga kasar sun bada labarin sojoji masu biyayya ga Mr. Gadhafi sun bude wuta da manyan makamai masu sarrafa kansu kan wani masallaci da ‘yan tawaye dake dauke da bindigogin adaka suke ciki. Masu adawa da gwamnatin sun kafa sansani a masallacin ne tun kwanaki d a suka wuce.

Sojojin sun ragargaza husumiyar masallacin da makaman harbe jiragen sama. Wata jaridar kasar Quryna ta bada labarin an kashe akalla mutane 23.Birnin dake kusa da gaba da matatun mai,Zawiya ne babban cibiyar manyan bututun daukar maid a iskar Gas a Libya.

Da yake magana ta woyar tarho da tashar talabijin na kasar,Shugaba Gadhafi wadda ke ci gaba da zama saniyar ware ko da cikin kasar,ya karkata jawabinsa ne kan mazauna Zawiya.Cikin jawabin mara kan gado,yace dakarun al-Qaida ne suka surka shayin matasan birnin da kayana maye,domin tada fitina. Ya yi kira ga jama’ar Zawiya su kare ‘yayansu. Kafofin yada labarai masu zaman kansu basu ga magamar al-Qaid a da boren d a ake yi a Libya ba.

Shugaban ya yi jawabin ne yayinda magoaya bayans asuka kai farmaki kan wata karamar tashar jiragen sama dake Misurata,birni na uku a girma aLibya,birnin mai tazarar kilomita metan daga birnin Tripoli ta gabashi.Amma mazauna birnin suka ce zuwa daren jiya Alhamis masu zanga zanga sun sake kame tashar jiragen. Ahalin yanzu kuma kamfanin dillancin labaran Associated Press yace wani dan uwa kuma mashawarci na kud da kud ga Gadhafi,Ahmed Gadhafil-Dam ya gudu zuwa Masar inda yake neman mafaka.