Gwamnatin Chadi ta dade tana goyon bayan manufofin kasashen yamma, tare da yin Allah wadai da matakin da Rasha ta dauka a baya-bayan nan a yankin Sahel na Afirka.
Kasar Rasha dai na yunkurin kawar da tasirin kasar Faransa da ta yi mulkin mallaka a yammacin Afirka da kuma yankin Sahel, tare da kulla alaka da kasashen da suka fada cikin rudanin juyin mulki tun shekarar 2020.
Deby dai ya jagoranci kasar Chadi tun a shekara ta 2021, lokacin da ya karbi mulki ta hanyar juyin mulki jim kadan bayan an kashe mahaifinsa Idriss Deby, wanda ya dade yana kan karagar mulki, a yakin da suka yi da 'yan tawaye masu adawa da gwamnati.
A cikin takaitaccen tsokaci da aka yi ta gidan talabijin, Putin ya ce Rasha ta ji dadin yadda Deby ya daidaita al'amura a kasar, kuma a shirye suke su taimaka ta kowace hanya.
A cewar wani kwafin da aka buga a shafin yanar gizon Kremlin, Putin ya ce kasashen biyu suna da "manyan damammaki don bunkasa alakar mu", kuma Rasha za ta ninka adadin da ake baiwa daliban Chadi da ke zuwa karatu a jami'o'in Rasha.
Ziyarar Deby ta zo ne mako guda bayan firaministan Nijar, wanda shi ma gwamnatin mulkin soja ta nada, ya ziyarci birnin Moscow.
A jamhuriyar Nijar da Burkina Faso, juyin mulkin ya haifar da gwamnatocin soji da suka balle daga Faransa inda su ka koma hulda da Rasha.
Tasirin Rasha a wasu kasashe ciki har da Mali da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, ya samo asali ne daga huldar da rundunar sojojin haya ta Wagner Group ta Moscow, karkashin jagoranci Yevgeny Prigozhin, ke yi da kasashen.
An kashe Prigozhin a wani hatsarin jirgin sama a watan Agustan da ya gabata, watanni biyu bayan da ya jagoranci kungiyar ta Wagner a wani yunkurin da bai yi nasara ba da nufin hambarar da manyan sojojin Rasha.
Tun bayan mutuwar Prigozhin, Rasha ta karbe ikon huldarsa a Afirka, tare da hada ayyukan Wagner a cikin tsarinta na yau da kullun.