Sakataren harkokin wajen Amurka, Mike Pompeo, zai gana da takwarorin aikinsa na kungiyar kasashen da ke yankin Kudu maso gabashin Asiya a Singapore da ake kira ASEAN, lamarin da ke nuni ga irin yunkurin da Amurka ke yi na ganin an samu kwanciyar hankali a tsakanin yankin tekun India a gefe guda da kuma na tekun Pacific a daya bangaren.
Sai dai akwai alamun da ke nuni da cewa, batun kasar Korea ta Arewa shi zai mamaye batutuwan da za a tattauna a taron.
A wannan taron koli na ministocin kasashen gabashin Asiya, Pompeo zai hadu da takwarorinsa 17, domin tattaunawa kan manyan matsalolin tsaro da ke barazana ga yankin, ciki har da batun barazanar da nukiliyan Pyonyang ke yi, da rikicin yankin tekun kudancin Asiya, da na ‘yan Rohingya da ke jihar Rakhine a kasar Myanmar, da batun tsaron rumbun adana bayanan sirri da sauransu.
A lokacin da aka tambaya ko Sakatare Pompeo zai gana da Ministan harkokin wajen Korea ta Arewa Ri Yong-ho a taron na Singapore, wani babban jami’in ma’aikatar harkokin wajen Amurka ya fadawa manema labarai cewa, “kasar ta Korea ta Arewa na zauren taron ne a matsayin mambar kungiyar ASEAN a tsakanin sauran mambobi 27, saboda haka, akwai tattaunawar da za a yi da ta shafi Korea ta Arewa.”
Shi ma Ministan harkokin wajen Iran, Mohammad Javad Zarif, zai kasance a taron, amma babban jami’in na ma’aikatar harkokin wajen Amurka ya ce babu wani shiri da aka tsara na tattaunawa da kasar ta Iran.