Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo, ya fito a fili jiya Lahadi, yace shugaba Donald Trump, yana shirin zai fice daga yarjejeniyar da manyan kasashen duniya tareda Amurkan suka kulla da Iran kan shirin Nukiliyar Farisan, muddin ba'a yiwa yarjejeniyar kwaskwarima ba, idan wa'adin sabunta shirin ya cika cikin watan gobe.
Pompeo, wanda a halin yanzu yake gabas ta tsakiya a ziyararsa ta farko kan wannan mukami a kasashen waje, yace shugaba Trump ya fito fili ya nuna cewa wannan yarjejeniya tana da rauni. Ya umarci jami'an gwamnatinsa suyi aiki domin inganta shi, kuma idan ba za'a yi hakan ba, to zai janye Amurka daga wannan yarjejeniya. Abu ne kai tsaye babu kumbiya kumbiya.
Da yake magana a Isra'ila, Pompeo yace ba kamar sauran gwamnatocin Amurka da suka wuce ba,shugaba Trump yana da ciakken shiri kan Iran, wadda aka tsara da nufin tunkarar jerin barazana da suke fitowa daga hukumomin kasar a Tehran.
A nata bangaren, Iran tace, bata da niyyar canja yarjejeniyar data kulla da kasashen Jamus,da Faransa, da Britaniya, da China da Rasha, da kuma Amurka,ta ko wace hanya ciki harda kulla wata sabuwa.