Poland Ta Kori Kocin Tawagar 'Yan Wasanta

Kocin Poland, Czesław Michniewicz.

A ranar 31 ga watan Disamba kwantiragin Michniewicz zai kare, kuma hukumar kwallon kafar kasar ta Poland ta ce ba za ta sabunta shi ba.

Hukumar kwallon kafar Poland ta sallami kocin tawagar ‘yan wasan kasar Czesław Michniewicz.

Poland ta sallami Michniewicz ne bayan da ta yi nazarin irin rawar da kungiyar ta taka a gasar cin kofion duniya da aka kammala a Qatar.

A ranar 31 ga watan Disamba kwantiragin Michniewicz zai kare, kuma hukumar kwallon kafar kasar ta Poland ta ce ba za ta sabunta shi ba.

A cewar kamfanin dillancin labarai na AP, Poland ta ce nan ba da jimawa ba za ta fara neman sabon koci.

Tawagar 'yan wasan Poland

Ko da yake, hukumar ta amince cewa, Michniewicz ya karbi ragamar tafiyar da kungiyar a wani lokaci mai sarkakiya, amma duk da haka ya cimma wasu nasarori.

Michniewicz ya kai tawagar ‘yan wasan ta Poland zuwa zagayen kwaf daya a gasar ta cin kofin duniya a karon farko cikin shekaru 36.

Sai dai hukumar ta ce akwai wasu karin batutuwa da ta yi la’akkari da su, wadanda suka sa ba za ta sabunta kwantiraginsa ba.