Al’ummar Irigwe dake karamar hukumar Bassa a jihar Filato sun bukaci gwamnatin tarayyar Najeriya da ta gudanar da bincike kan kashe-kashen dake aukuwa a yankin da zummar gano masu laifi domin a hukumtasu.
Taron manema labarai da Kungiyar Raya Al’adun Irigwe ta kira, ya biyo ne bayan kisan wasu mata da yara 29 da wasu ‘yan bindiga suka yi ranar Litinin.
Shugaban kungiyar Mr. Sunday Abdu yace kisan mutanen ya auku ne a wurin da sojoji ke gudanar da aikin tsaro a yankin. Yace a dakin da sojoji suka ba mutanen mafaka ne ‘yan bindigan suka shiga suka kashesu. Mr. Abdu yace kowane mako ana kashe masu mutane tare da kone gidajensu. Yace su kam suna ganin dokar hana fita da dare da aka kafa, bata yi tasiri ba.
Ga rahoton Zainab Babaji da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5