Maharin da ya kai hari kan wajen wani ibadan Yahudawa ya kashe mutum 11 a birnin Pittsburg ya yi bayyanarsa ta farko a gaban kuliya.
Robert Bowers ya bayyana ne a gaban kotun Magistrate akan keken guragu sa'o'i kadan bayan da aka sallamo shi daga asibiti sanadiyar harbin da 'yan sanda suka mai kafin su kama shi.
An daga saurar karar zuwa ranar Alhamis mai zuwa inda ake sa ran masu shigar da kara za su fara gabatar da hujjoji akan Bowers.
Gabanin haka kuma, dubban mutane sun hadu jiya Lahadi a birnin Pittsburgh na jihar Pennsylvania da ke Amurka a wajan tunawa da wadanda suka rasa ransu a harin.
Wata kungiya da take yaki da kyamar Yahudawa, wacce kuma take yin nazarin kiyayya da tashin hankali da ake nunawa yahudawa tun daga shekarun 1970, ta ce kisan da aka yi a wajan bautar Yahudawa shi ne hari mafi muni da aka taba kai wa akansu a tarihin Amurka.