Da yake jawabi ga wasu jami’an gwamnati da aka nada akan sababbin mukamai a jiya Litinin, shugaba Rodrigo Duterte ya dora laifi a kan Amurka cewa dalilinta ne mayakan Musulmin ke tada kayar baya a yankin. Wannan shine karo na farko da ya fito ya bayyana adawarsa ga zaman da sojojin Amurka suke yi a kasarsa.
Sai dai shugaba Duterte bai kayyade lokaci da yakamata sojojin Amurka su bar kasar ko kuma yanda za a tafiyar da shirin janyewarsu ba, sai dai yace Amurkawan sune wadanda kungiyoyin ta’addancin masu nasaba da Abu Sayyaf ke nema kuma dalilinsu ne yan ta’addan suka kara kaimi.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Amurka John Kirby yace basu da wani labari a hukumance daga gwamnatin Philippines a kan wannan batu.
Sanarwa ta shugaba Duterte a jiya ta zo ne mako daya bayan wasu kalamai marasa dadi da yayi ga Amurka da shugaba Barrack Obama a Laos, wanda yayi sanadiyar Obama ya soke ganawarsu a wurin taron. Amma dai karshenta daga bisani shugabanni biyu sun hadu a wurin taron kolin.