Mai magana da yawun ma’aikatar tsaron Moon Sang-gyun, ya ki bayar da ‘karin bayanan da suka wuce na cewa gwajin zai iya faruwa a wata hanyar ‘karkashin ‘kasa a Punggy-ri, inda Koriyar ta Arewa tayi gwajin makamanta a baya, a kokarinta na kirkirar makamin Nukiliya da zai iya shiga makamanta masu linzami.
Gwajin na baya bayan nan ya faru ne ranar Juma’a. wanda shine na biyar kuma mafi girma da Koriyar ta yi.
Kwamitin tsaro na MDD yayi Allah wadai da gwajin, yana mai cewa ya keta ka’idojin takunkumin da aka kakaba sakamakon ire iren gwaje gwajen makaman Nukiliya da ta yi a baya. Kwamitin dai yayi alkawarin daukar makatakan da suka kamata a wata sanarwar da ya fitar.