Tsohon dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa na Liverpool, da Tottenham, Peter Crouch, mai shekaru 36, da haihuwa yakafa tarihi a faggen kwallon kafa.
Peter Crouch, ya zamo dan wasan da yafi kowani dan wasa jefa kwallaye a raga da kai a Kasar Ingila, bangaren firimiya lig.
Domin ya samu nasarar zurara kwallaye da kai har sau 51, a wasannin daban daban da ya buga wa kungiyoyin kwallon kafa daban daban da suke buga firimiya lig na kasar Ingila.
Dan wasan ya haura yawan kwallayen da tsohon dan wasan gaba na Newcastle United, Alan Shearer, ya jefa raga da kai wanda a zamaninsa ya jefa kwallaye 46, duk da kai a gasar firimiya lig kafin ya rataye takalmansa na taka leda a shekara ta 2006.
Peter Crouch, ya cika kwallonsa na 51, da yaci da kai ne a wasan da kungiyarsa ta Stoke City tayi da takwararta ta Southampton na gasar firimiya lig na bana mako na takwas Inda Stoke city ta doke ta 2-1.
Dan wasan mai shekaru 36, a duniya ya buga wasannin a kungiyoyin kwallon kafa da dama kafin yazo kungiyar Stoke City a shekara ta 2011, daga kungiyar Tottenham, na Kasar Ingila.
Ya buga wasanni har guda 176 wa kungiyar Stoke city ya kuma samu nasarar jefa kwallaye guda 42 a raga a wasannin daban daban da ya fafata wa Stoke city.
Your browser doesn’t support HTML5