Pelosi: Shugaban Amurka Trump, Bashi Da Tarbiyya Ko Kamun Kai

Kakakin Majalisar dokokin Amurka Nancy Pelosi

Kakakin majalisar dokokin Amurka Nancy Pelosi, tace maganar tsige shugaban Amurka Donald Trump, bai kai abun dubawa ba, don a cewarta, “shugaban bai isa ma a bata lokaci a kansa ba.”

A wata hira da tayi da jaridar Washington Post da aka wallafa jiya Litinin, Pelosi tace shugaba Trump bai can-canci zama shugaban kasar ba, don bashi da tarbiyya, kamun kai da kuma basirar da suka dace da mukamin ba.

Amma yanzu da majalisar da ‘yan jam’iyyar Democrats ke jagoranci suka kaddamar da kwamitocin bincike iri-iri, akan yakin neman zaben Trump da harkokin kasuwancinsa.

Pelosin ta amsa tambaya akan kiraye-kiraye da akeyi na neman tsige shugaban kasar, inda da tace tana ganin hakan ba alheri bane ga kasar, kuma zai iya janyo rabuwar kawunan mutanen kasar.

Tace yanzu hankalin ta yana kan zaben 2020 ne wanda suke fatar ganin ‘yan jam’iyyar su ta Democrat sun kwaje majalisar dattawa, kai harma da fadar shugaban kasar White House.