PDP Ta Musanta Zargin Da Gwamanan Kano Yayi

Gwamnan jihar Kano, Dr. Rabi'u Musa Kwankwaso

Gwamanan Kano Dr Rabiu Kwankwaso yayi zargin cewa gwamnatin tarayya tana shirya wata makarkashiya ta ganin bayansa amma jam'iyyar PDP reshen Kano ta musanta zargin.
Kwana kwanan nan wasu kafofin labaru suka ruwaito gawamnan Kano Dr Rabiu Kwankwaso na cewa fadar shugaban kasa na shirya wata makarkashiyar ganin bayan rayuwarsa.

A cikin wata fira ta musamman da jaridar Freedom Times gwamnan yace akwai managarcin dalilai da hujjoji a wurinsa wadanda ke cewa lallai shugaba Jonathan na kokarin hallakashi inda ma ya bada misali da rage adadin jami'an tsaro dake tsaron lafiyarsa a gidan gwamnati.

Amma jam'iyyar PDP reshen Kano ta mayar da martani game da zargin da gwamnan yayi. Alhaji Yahaya Umar Bagobiri mataimakin shugaban kwamitin riko na jam'iyyar yace kalaman gwamnan kuskure ne ga kasa musamman ga al'ummar jihar Kano. Yace idan yana da wani abu da yake gani ba daidai ba ai shi da shugaban kasa kamar wa ne da kani. Yakamata ya je wurin shugaban kasa ya shaida masa abubuwan dake damunsa.

Amma abun dake faruwa inji Alhaji Bagobiri gwamnan Kano baya jin shawarar dattawan jihar Kano da manya-manyan malamai da duk mutane masu mutunci da daraja a jihar Kano. Yana yin abubuwa na mulkin kama karya.

Akan zargin da gwamnan yayi cewa PDP ke kokarin tayar da tarzoma a Kano tun lokacin da gwamnan ya fita daga jam'iyyar kuma da nadin sabon sarkin Kano sai Alhaji Bagobiri yace ko kadan babu hannun jam'iyyar PDP ko wani abu da zai nuna tana kokarin tada hargitsi. Yace idan ma akwai ai su ma 'yan PDP al'umma ce a jihar. Jama'ar jihar Kano basa goyon bayan abun da gwamna yayi musamman sabon sarkin da ya nada.

Akan cewa babu abun da ya shafi PDP da batun masarauta da kuma nadin sabon sarki sai Alhaji Bagobiri yace sarkin da ya rasu yayi abubuwa na gina al'ummar jihar Kano. Yayi kokari wurin samar da zaman lafiya. Yayi kokari wurin tabbatar da habbaka addinin Musulunci da kuma zaman lafiyar jihar Kano.

Akan rage jami'an dake tsaron lafiyar gwamnan Alhaji Bagobiri yace su basu da masaniyar lamarin. Idan yana ganin abun da ba daidai ba shugaban kasar Najeriya abokin aikinsa ne. Yakamata yayi tattaki zuwa wurinsa ya shaida masa, amma ba ya fito yana maganganu a matsayinsa na shugaba ba. Yace kuskure ne kuma ya yiwa jama'ar Kano ba daidai ba.

Yanzu dai 'yansanda kalilan ne ke gidan gwamnati sai kuma 'yan sa kai masu rike da sanduna da kulake.

Ga rahoton Mahmud Kwari.

Your browser doesn’t support HTML5

PDP Ta Musanta Zargin Da Gwamnan Kano Yayi - 4'15"