Yayinda jam’iyyar PDP ke cewa ba zata lamunta da cin zarafin gwamnan Ekiti ba da ta ce ‘yan sandan jihar sun yi,jam’iyyar APC cewa ta yi ba akidar shugaba Buhari ba ne a ciwa wani zarafi domin ya ci zabe. Hukumar ‘yan sandan jihar Ekiti ta musanta zargin mamaye gidan gwamnatin jihar
Jam’iyyar PDP ta nuna kaduwa da yadda ta ce ‘yan sanda sun ci zarafin gwamnan Ekiti, Ayo Fayose gabanin zaben gwamnan jihar ranar Asabar.
An nuna hoton Fayose kamar yana kuka saboda ya shaki barkonon tsohuwa na ‘yan sanda har ma ya nuna an yi masa rauni a wuya. Jam’iyyar ta ce sam ba zata lamunce da hakan ba tare da zargin cewa APC na neman murde zaben ne.
Sanata Umar Tsauri sakataren jam’iyyar ya ce idan har ‘yan sanda zasu zagaye gidan gwamnan dake kan gado yanzu, sun yi masa duka, tamkar dimokradiya a Nigeria ta zo karshe ke nan.
Shi ma shugaban PDP na arewa maso yamma Ibrahim Kazaure y ace jam’iyyarsu ce ke da rinjaye a jihar Ekiti. Yace PDP zata ci zaben sai dai a kwace mata. Idan an kwacewa PDP zabe a jihar Ekiti shi ne zai zama tushen rikici a Nigeria.
Amma APC ta bakin mataimakin shugabanta na arewa maso gabas Mustapha Saliu yace ba dabi’ar shugaba Buhari ba ce kawar da kai daga masu cin zarafin jama’a. Yace akoda yaushe shugaban kasa na fada masu baya son a ci zarafin mutane domin shi ya ci zabe. Shugaban kasa y adage akan cewa dolea yi adalci a yi zabe ba tare da ciwa kowa mutunci ba.
Daga jihar Ekiti rundunar ‘yan sada ta musanta mamaye gidan gwamnati. Ta ce sam bata yi haka ba.
A saurari rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya
Your browser doesn’t support HTML5