Alkawarin gwamnatin tarayyar najeriya ta Jam’iyyar APC na rarraba naira dubu biyar-biyar ga masu rangwamen karfin aljihu da batun sarrafa dala miliyan 322 a tsakanin matalautan kasar da kuma shirin gwamnatin Jigawa na raba a kalla naira dubu 50 ga kowane akwatin zabe a fadin jihar kuma a kowane watan duniya, duka matakai ne rage radadin fatara da talauci a tsakanin talakawa a cewar gwamnatocin.
Sai dai tuni masu nazari ilimin kimiyyar siysa da shugabanci na gari ke kushe waannan tunani.Dr Sai’idu Ahamd Dukawa na Jami’ar Bayero, Kano, yace babu wani wuri a tsarin ilimantarwa ko kuma bunkasa al'umma da ya bada damar rabawa al'umma tsabar kudi idan ba domin tallafawa harkokin ilimi ba.
A watan jiya ne dai gwamnatin Jigawa ta fara aiwatar da shirin ta na raba kudade a akwatinan zabe fiye da dubu 3 a fadin jihar bayan da shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar da shi a watan mayu.
A karkashin shirin an tsara samar da a kalla naira dubu 50 ga kowane akwati a duk karshen wata.
To amma a iya cewa, shirin ya fara gamuwa da cikas, inda a litinin din nan, wasu matasa suka lakadawa shugaban karamar hukumar Dutse duka kuma sukayi garkuwa dashi a ofishinsa, bisa zargin ya zauna akan irin wadancan kudade na akwati.
Comrade Kabiru Sa’idu Dakata daraktan kungiya CAJA masu rajin habaka rayuwar al’uma ya yi tsokaci a kan batun, yace ajiye matashi mai karfi a jika a bashi Naira dubu biyar biyar ba sana'a aka nemi koyawa mashi da hanyar dogaro ga kai ba, ba zai taimaka ba. yayyana cewa wannan zai kara bada damar cin hanci ne kawai amma ba zai yi maganin talauci ba.
A talatar nan ce dai majalisar dokoki ta Jigawa ta dakatar shugaban karamar hukumar ta Dutse tsawon watanni 6, biyo bayan wancan zargi da matasan sukayi akan sa na almundahanar kudin akwati.
Ga Rahoton da Mahmud Ibrahim Kwari ya hada mana.
Facebook Forum