PDP Ta Yi Allah Wadai Da Matakin Rufe Twitter A Najeriya

Gwamnonin PDP a wani taro da suka yi kwanan nan a kudancin Najeriya (Twitter/ PDP)

PDP ta kwatanta matakin a matsayin “mulkin kama karya wanda ya dora kasar kan turbar shugabanci irin na danniya.”

Babbar jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta soki matakin da hukumomin kasar suka dauka na rufe kafar sada zumnta ta Twitter.

A ranar Juma’a ministan yada labarai Alhaji Lai Mohammed ya bada umurnin rufe kafar, kamar yadda mai taimaka masa na musamman Segun Adeyemi ya fitar a wata sanarwa.

"Jam’iyyar PDP na watsi da wannan mataki mara kan gado, na dakatar da kafar sada zumunta ta Twitter.” Wata sanarwa da kakakin jam’iyyar Kola Ologbondiyan ya fitar ta ce.

PDP ta kwatanta matakin a matsayin “mulkin kama karya wanda ya dora kasar kan turbar shugabanci irin na danniya.”

Sanawar har ila yau ta ce, dakatar da kafar ta Twitter, yunkuri ne na tankwasa ‘yan Najeriya musamman matasa, don kada su binciki ayyukan gwamnati, tana mai cewa, matakin tamkar take hakkin bil adama ne.

“Jam’iyyarmu ta kadu da matakin da gwamnatin tarayyar ta dauka wanda ya yi kama da mataki da za a dauka a zamanin da, saboda kawai kamfanin sada zumuntar ya bi ka’idojin kasa da kasa, wajen hana gwamnatin Buhari yin amfani da Twitter don nuna kiyayya ga ‘yan Najeriya.”

Gwamnati ta ce ta dauki matakin ne, saboda amfani "ana yawan amfani da shafin wajen gudanar da wasu ayyukan da ka iya yin barazana ga zaman lafiyar Najeriya."

Sai dai jama'a da dama na ganin matakin, bai rasa nasaba da goge wani sakon Buhari da kamfanin na Twitter ya yi a ranar Laraba, saboda a cewar kamfanin ya saba ka'idar shafin.