Jami’iyyar PDP a jahar Filato ta umarci gwamnan jahar, Simon Lalong, da ya gaggauta gudanar da zabe a kananan hukumomi hudu na shiyar arewacin jahar.
A makon jiya ne gwamna Lalong ya rantsar da shugabannin riko a kananan hukumomin Jos ta Arewa, Jos ta kudu, Riyom da Barikin Ladi, shekara guda bayan an gudanar da zabe a sauran kananan hukumomin jahar.
A taron manema labarai da shugabannin jami’iyyar su ka kira, kakakin jami’iyyar PDP a jahar Filato, John Akans, ya ce rashin gudanar da zabubbuka a kananan hukumomin rashin adalci ne da kama karya.
Mataimakin shugaban jami’iyyar PDP a shiyyar arewacin jahar Filato, Chris Hassan, ya ce hujjan da gwamnan ya bayar na rashin tsaro a yankin, sam ba gaskiya ba ce.
Itama shugaban mata ta jami’iyyar PDP a jahar Filato, Matina Dakup, ta ce lauyoyinsu na kan nazarin basu shawarwari kan matakan da za su dauka.
Sai dai a martanin da Sakataren jami’iyyar APC na jahar Filato, Bashir Musa Sati, ya ce abinda ake bukatar shine a samu wanda zai kawo ci gaba a jahar.
Saurari cikakken rahoton wakiliyarmu Zainab Babaji daga Jos:
Your browser doesn’t support HTML5