Shugaban babbar jam’iyyar adawa ta PDP a jihar Kaduna, Mr. Felix Hassan Hyat, ya fadawa taron manema labarai cewa, an kama jigajigan jam’iyyar a jihar tare da hadin bakin jam’iyya mai mulki ta APC, inda aka tafi da su Abuja.
Ya kuma kara da cewa suna zargin za’ayi amfani da sojoji da kuma 'yan kato da gora domin a haddasa rigima saboda mutane su ji tsoro, yana mai cewa, wadannan ba hanyoyin dimocradiyya ba ne.
Amma a nata bangaren jam’iyya mai mulki ta APC a jihar, ta mayar da martani ta hannun mataimakin mai magana da yawun jam’iyyar APC, Alhaji Salisu Tanko Solo, wanda ya ce, shugaban jam’iyyar PDP na jihar ya kasa fadawa jama’a dalilin da ya sa aka kama su.
Inda ya kara da cewa ko shi ya yi irin wadannan kalaman batanci to yana gayyatar jami’an tsaro su kama shi, saboda kalaman da su ka yi hankali ba zai dauka ba.
Saurari cikakken rahoton Isah Lawal Ikara:
Your browser doesn’t support HTML5