PDP Ta Daukaka Kara Zuwa Kotun Koli Bayan Nasarar Buhari A Kotu

Atiku Abubakar

Babbar jam'iyyar adawar Najeriya PDP da dan takarar ta Atiku Abubakar sun daukaka kara zuwa kotun koli kan hukuncin kotun shari'ar zaben 2019 da ya tabbatarwa Shugaba Muhammadu Buhari nasarar zaben.

Babban lauya a tawagar lauyoyin jam’iyyar PDP, Mike Ezekhome, wanda tun farko ya ba da tabbacin za su daukaka kara, ya ce sun mika wa kotun kolin hujjoji 66 da su ka hakikance za su iya ba su nasarar karar.

Ezekhome bai bayyana jerin hujjojin ga manema labaru ba, amma an fahimci akwai batun nan na zayyana takardun kammala karatun Shugaba Buhari da aka mika wa hukumar zabe ba su da sahihanci.

Hakanan PDP na kalubalantar hukumar zabe kan batun na'urar aika sakamakon zabe ta na'ura mai kwakwalwa da ta ke cewa da dai za a bi alkaluma ita ta lashe zaben.

Kakakin kamfen na jam’iyyar PDP, Buba Galadima, ya ce sun sake yunkurin bin matakan shari'a kan sakamakon zaben da ba su amince da shi ba.

Ana ta bangaren jam'iyyar APC ta bakin sakataren walwala, Ibrahim Masari, ta ce ba ta shakkar daukaka karar don ta na da yakinin shugaba Buhari ne ya lashe zaben.

Batun da wasu kafafen labaru na yanar gizo su ka yada da ke nuna jam’iyyar APC ma ta shigar da wata karar daban ta neman soke wasu daga korafe-korafen jam’iyyar PDP a karar, bai samu tabbacin hakan ya faru daga jam'iyyun ba.

Saurari cikakken rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya daga Abuja:

Your browser doesn’t support HTML5

Katun Koli: PDP Ta Daukaka Kara Tana Kalubalantar Nasarar Zaben Buhari