Paparoma Ya Yi Addu’a Ga Mutum 37 Da Suka Rasa Rayukansu A Hare-haren Najeriya

Your browser doesn’t support HTML5

Paparoma Francis ya yi wa wadanda suka rasa rayukansu da wadanda suka jikkata addu’o’i bayan wani hari da aka kai kan wasu kauyuka da ya halaka mutum 37 a Najeriya.
Paparoma Francis ya yi wa wadanda suka rasa rayukansu da wadanda suka jikkata addu’o’i bayan wani hari da aka kai kan wasu kauyuka da ya halaka mutum 37 a Najeriya.

Yayin da yake jawabi a taron addu’o’i da yake jagoranta na mako-mako a Fadar Vatican, Paparoma ya ce “cikin yanayi mai kona rai, na samu labarin tashin hankalin da ya faru a arewacin kasar da ke nahiyar Afirka.”