Paparoma Francis Ya Yada Zango a Bolivia

Paparoma Francis a Bolivia

A ci gaba da ziyarar da ya kai a yankin kudacin Amurka, shugaban mabiya darikar katolika na duniya, Paparoma Francis, ya yada da zango a kasar Bolivia a yau Laraba.

Kafin ya isa kasar ta Bolivia, Paparoman ya kai ziyara kasar Ecuardo, inda ya yi kira ga al’umar kasar da su dinga tallafawa talakawa, tare da kokarin kare muhalli domin al’umomi masu zuwa.

A wani jawabi da ya yi a gaban shugabannin kungiyar ‘yan kasuwar kasar da kuma ainihin mazauna birnin Quito, Paparoma ya bayyan cewa, albarkatun kasa na kowa-da-kowa ne.

Wannan jawabi kan kare muhalli, ya kasance na farko, tun bayan da Paparoman, ya fitar da wata mukala a watan da ya gabata, inda ya yi kira ga shugabannin kasashen duniya, da su dauki matakan gaggawa domin dakile matsalar sauyin yanayi da ake fuskanta, tare da kawo karshen dogaro da ake yi akan man fetur.

Paparom dai ya sha suka kan wannan matsaya da ya dauka daga masu adawa da batun sauyin yanayi, musamman ma a nan kasar Amurka, wacce ya ke shirin kawowa ziyara a watan Satumba mai zuwa.