Ministan Harkokin Wajen Pakistan, Sha Mahmood Qureshi, ya fada, gabanin ziyarar da zai kai Amurka wannan satin cewa da yiwuwar ita da Amurka zasu cimma matsaya game da batun likitan nan da Pakistan ta jefa gurkuku saboda taimaka ma Amurka da ya yi ta samu ganowa da kuma kashe Osama bin Laden.
WASHINGTON D.C. —
Zuwa yanzu dai jami'an Pakistan sun yi watsi da duk yinkurin Amurka na ganin an saki Dr. Shakeel Afridi, wanda aka yanke masa hukuncin dauri mai yawa bayan da ya taimaka ma sojojin kundunbalar Amurka su ka gano gidan da su ka kashe bin Laden a garin Abbottabad a shekarar 2011.
An kai farmakin ne a cikin kasar Pakistan ba tare da sanin gwamnatin kasar ba, al'amarin da ya zama abin kunya ga hukumomin kasar har ya kai ga daure Afridi, wanda hakan kuma ya janyo takaddama tsakanin Amurka da Pakistan.