Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Anyi Girgizar Kasa Da Tsunami A Indonesia


Mazauna Palu dauke da gawar wani da Tsunami ta kashe a Palu, Central Sulawesi, Indonesia,, Sept. 29, 2018.
Mazauna Palu dauke da gawar wani da Tsunami ta kashe a Palu, Central Sulawesi, Indonesia,, Sept. 29, 2018.

Jami'an agaji na kungiyar Red Cross sun ce babu wani bayani da suka ji daga Donggala kuma hakan ya sa su damuwa matuka. Sakamakon akwai mutane kimanin 300,000 dake zaune a wurin.

Kamar yadda jami’ai a Indonisiya ke fadi, adadin mutanen da suka rasu sakamakon masifar girgizar kasa da Tsunami a Indonisiya ya ninka har sau biyu, inda yawan mutanen da suka mutu yakai 832, sai 540 da suka jikkata.

Wannan adadin mutanen da suka mutu na birnin Polu ne kawai sakamakon har yanzu babu wani cikakken bayani daga Donggala.

Kamar yadda kafar yada labarai ta Faransa ta rawaito, Mai magana da yawun Hukumar agajin gaggawa da masifu ta Indonisiya, Sutopo Purwo Nugroho na cewa “a yau Lahadi zamu fara binne matattun saboda tsoron yaduwar cututtuka.”

Mummunar girgizar kasar wacce a ma’aunin girgizar kasa na magnitude ta kai 7.5 ta afku ne a ranar Juma’a, wacce tayi sanadiyyar ambaliyar ruwa ta Tsunami, da ta afkawa birane biyu na Palu da Donggala wadan da ke tsakiyar shiyyar Sulawesi.

Jami’ai sunce a ranar Asabar mutane da yawa na bakin tekun Palu domin halartar taron kalankuwa a lokacin da girgizar kasar ta afku, sakamakon haka igiyar ruwa mai karfi ta tafi da mutane masu yawa.

Nugroho yace ambaliyar ta Tsunami ta ingizo ruwa mai tafiyar kilomita 800 a cikin awa daya, wanda ya ruguje gine gine. Ya kara dacewa dubban gidaje da asibtoci da kasuwanni da otal otal sun ruguje haka kuma zabtarewar kasa ta raba babbar hanyar Palu.

Wata babbar gada da ta ratsa gefen tekun shiyyar Sulawesi ta karye.

Shugaban Indonesiya Joko Widodo ya isa birnin Polu a yau lahadi, daya daga cikin biranen da masifar ta afkawa domin duba irin barnar da ta afku da kansa.

Shugaban yayi wa dakarun da aka aika wurin jawabi, inda yace su shirya yin aiki babu dare babu rana.

Kusan mutane dubu 17,000 ne suka yi hijira a wani sansanin wucin gadi a cewar hukumar kula da masifu ta kasar Indonisiya.

Indonesia dai na daya daga cikin kasashen da suka fi kawanne fuskantar masifu a duniya. Sakamakon kasar ta na yankin da ake wa lakabi da Zoben wuta, yankin da ke kewaya da duwatsu masu aman wuta kuma, kasar wurin bata da karfi sakamakon Tekun Pacific.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG