A yau Laraba Firai Ministan Pakistan, Imran Khan, ya yi gargadi ga India akan matakin da ta dauka kwanan nan da ya janyo ce-ce-kuce a Jammu da kuma Yankin Kashmir da yake barazana ga zaman lafiyar yankin.
Khan ya bayyana hakan ne a lokacin da kasar take bikin samun ‘yan cin kai, sama da mako guda bayan da India ta dauki matakin soke kwaryakwaryar cin-gashin- kai da ta bai wa wani bangare da aka raba na Yankin Himalayan.
Sai kuma Gwamnatin India ta sake tura dubban karin sojojinta da kuma saka miliyoyin mutanan Yankin na Kashmir jami’an tsaro da ba’a taba gani ba don kwantar da tashin hankalin da ka iya tashi.
Amma duk da haka, tuni aka samu wasu rahotanni da ke cewa an saukakawa mutane matakan da aka dauka masu tsauri.
A cewar Khan, “ranar samun ‘yan cin kai wata dama ce da za mu nuna farin cikinmu, amma yau muna cikin bakin ciki na yanayin da ‘yan uwanmu na Yankin Kashmir da aka mamaye a Jammu da kuma Kashmir wadanda India take cin zalinsu.”