Oumarou Noma Ne Shugaban Jam'iyyar Moden Lumana - Kotu

Tambarin jam'iyar Moden Lumana

Wata kotu a birnin Yamai da ke Nijar ta bayyana hukuncin da ta yanke a shari’ar da ta hada bangarorin da ke rikicin shugabancin jam’iyar Moden Lumana ta tsohon Frai Minista Hama Amadou.

Kotun ta jaddadawa Oumarou Noma matsayinsa na shugaban jam'iyyar bayan rikicin siyasar cikin gida ta sa aka tsige shi a bara.

Tuni dai bangaren da kotun ta baiwa gaskiya ya fara kiran ‘ya'yan jam’iyar da su hada kai domin tunkarar zaben da ke tafe.

A shekarar da ta gabata ne wasu jiga-jigan jam’iyyar ta Moden Lumana suka tsige shugaban rikon kwaryar jam’iyyar Oumarou Noma daga mukaminsa don maye gurbinsa da Alhaji Tahirou Garba.

Oumarou Noma

Lamarin ya sa Noma ya garzaya kotu saboda a cewarsa matakin ya sabawa dokokin jam’iyya.

Bayan shafe watanni tana nazari akan wannan takaddama kotun ta bayyana Oumarou Noma a matsayin halitaccen shugaba, abin da ya matukar faranta ran magoya bayansa.

"Alhamdulillahi, mun gode wa Allah Ubangiji da ya gwada mana wannan rana, sakamako na lumana Allah ya ba Oumarou Noma gaskiya" In ji Alhaji Yaye, mai magana da yawun Noma.

A wani takaitacen jawabin da ya yi jim kadan bayan bayyanar wannan hukunci Oumarou Noma ya bukaci ‘yayan jam’iyyar da su hada kansu domin tunkarar zabubbuka masu zuwa.

Yayin da yake mayar da martani kan wannan hukunci, Mahamadou Mai Duka, wanda mamba ne a kwamitin kolin gudanar da jam'iyyar ta Lumana kuma daya daga cikin 'yan bangaren da suka sha kaye ya ce, "wannan sakamako, ni a nawa gani, zai karawa siyasar Lumana karfi."

Ainihin shugaban jam’iyyar Moden Lumana, Hama Amadou ne ya nada Oumarou Noma a matsayin shugaban rikon kwarya lokacin da yake hijira a waje kafin daga bisani ya aiko da wata wasikar da ta tsige shi daga mukaminsa.

Dalilin da ya janyo Oumarou Noma ya shigar da kara a kotu domin a cewarsa tsohon frai ministan ba shi da ‘yancin tsoma baki a sha’anin siyasa sakamakon hukuncin da aka yanke masa a game da shari’ar nan ta badakalar jarirai.

Saurari cikakken rahoton a cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

Oumarou Noma Ne Shugaban Jam'iyyar Moden Lumana - Kotu