Onitsha: 'Yan Sanda Sunyi Bayani Kan Fashewar Tankar Man Fetur

Onitsha Tankar Man Fetur

Onitsha Tankar Man Fetur

A garin Onitsha dake jihar Anambara, rundunar 'yan sandan jihar ta fito da bayani kan fashewar wata tanka mai dauke da man fetur jiya Laraba, wacce ta yi sanadiyar mutuwar mutane biyu da kuma qonewar shaguna da dama.

Wakilin Muryar Amurka Alphonsus Okoroigwe yayi hira da wasu mazauna grin Onitsha domin jin ta bakinsu yadda suka ga za'a magance hatsarorin da fashe-fashen tankoki masu dakon man fetur ke haddasawa.

Cynthia Erere daya daga cikin wadanda suka bada ra'ayinsu, tace ya kamata gwamnatin ta sa direbobin tankokin man fetur jigila da daddar, a hana su jigilar daukan man fetur da rana, domin yanayin da kan jefa rayukan al'umma cikin hadari. Yanzu haka mutane sun mutu, kuma an yi asarar dukiyoyi, kuma 'yan kasuwa da yawa sun shiga wani hali.

A saurari cikakken rahoto daga wakilin Muryar Amurka Alphonsus Okoroigwe.