Olympics: 'Yan Ninkayar Amurka Na Cin Karensu Ba Babbaka

Rio Olympics Swimming

Ana sa ran Michael Phelps da Katie Ledecky da ke jagorantar ‘yan wasan Amurka a gasar wasannin Olympics, za su ci gaba da nuna bajintarsu a yau Juma’a, inda suka mallake mafi yawan kyautar zinare a bangaren masu ninkaya.

A jiya Alhamis Phelps ya lashe kyautar zinare ta baya-bayan nan a ninkayar mita 200, yau kuma zai yi takara ne a ninkayar mita 100.

Ita kuwa Ledecky wacce sabuwar shiga ce a gasar ta Olympics, za ta kara a ninkayar mita 800.

Idan kuma har ta samu nasara, hakan na nufin ta lashe baki dayan karawar da aka yi a ninkayar mita 200 da 400 da kuma 800 a gasar wasannin da ake yi a birnin Rio na Brazil.

Shi kuwa Phelps, idan har ya samu nasara a karawar ta yau, hakan zai ba shi damar samun kyautar zinare ta uku ke nan a wannan gasa, kuma zinare na 23 a baki dayan wasannin Olympics da ya halarta a rayuwarsa.