Okasha Auwal Ibrahim, wanda aka fi sani da 'Big Star' wanda ya fara waka sakamakon ya taso inda ya riski 'yan uwansa matasa na waka irin ta Free Style, wato waka irinta Titsiye, daga nan ne ya fuskanci cewar waka ta na jininsa.
Ko da ya fara waka kamar kowa, ya samu ‘yar tangarda inda iyayensa basu lamunta ba da farko, sun yi tunanin ba abu ne mai kyau ba, a tunaninsu sun zaci cewar dan su ya dauko hanyar lalacewa.
Daga baya suka aminta suka kuma bashi damar yin waka, duk kuwa da cewar har kawo yanzu bai kammala karatunsa na sakandire ba, kuma ya ce yana bawa kowanne lokacinsa, lokacin karatu daban haka nan ma lokacin waka daban.
Ko da yake mafi yawan wakokinsa sun fi maida hankali kan sakonnin fadakarwa, mussaman ma ga matasa 'yan uwansa, ta bakin Okasha duniya idan ba’a bi ta a sannu ba zata kai mutum ta baro ne.
Ya ce gwarzonsa a mawaka shi ne Classic wanda ke da salo irin wanda yake so dangane da yadda yake wakokinsa.
Your browser doesn’t support HTML5