Reilly Knop, wata malamar da gwamantin Amurka ta aika Jamuhuriyar Niger domin yiwa kasarta hidima, ta shafe watanni 10 tana karantarda turancin ingilishi a makarantun ESCAE da IFTIC da koyas da matasa ilimin sana'o'i a kauyuka.
Reilly ta bayyana yadda take jin alamun za ta yi kewar dalibanta da ma sauran abokan aikinta, saboda a cewarta tayi zaman mutunci da su a tsawon lokaci da ta yi ta na aiki dasu.
Lura da yadda wannan matashiya ta gwada kwarewa akan aiki da kuma yadda ta zauna lafiya da jama’ar dake tare da ita, ya sa ofishin jakdancin Amurka a Yamai, shirya wata kwarya-kwaryar buki, domin bata damar yiwa abokan zamanta bankwana a hukumance inji Alhaji Idi Barau jami’in hulda da manema labarai na ofishin jakadancin Amurka a Niger.
A cewar Abba Kyari, wani malami dake koyarwa a makarantar IFTIC sun koyi abubuwa da dama daga Reilly Knop, a tsawon watanni 10 na aikin hidimar da ta yiwa Niger da sunan gwamnatin Amurka.
Shekaru sama da 30 kenan da cibiyar raya al’adun Amurka ke karantar da turancin ingilishi a Niger, abinda ya baiwa dubban jama’a, galibinsu matasa, damar lakantar karatu da rubutun wannan harshe da a yau suke amfana da shi a harkokinsu na yau da kullum. Saboda haka jakadan Amurka a Niger Ambassador Eric P. Whitaker, ya kara jaddada ci gaban wannan shiri na horasda jama’a.
A saurari rahoton Souley Barma domin karin bayani
Your browser doesn’t support HTML5