Obaseki Ya Sha Alwashin Zakulo Wadanda Suka Kashe Kanin Sowore, Atiku Ya Nuna Takaicinsa

Obaseki, hagu, Atiku Abubakar, dama (Facebook/KInstagram/ Atiku Abubakar/Godwin Obaseki)

Hukumomin tsaro sun ce ‘yan bindigar da suka kashe Olajide sun sace wasu mutane biyar da suke tare da shi.

Gwamnan jihar Edo Godwin Obaseki a Najeriya, ya lashi takubin kamo wadanda suka kashe Olajide Sowore, kani ga mawallafin jaridar Sahara Repoters, Omoleye Sowore.

A ranar Asabar wasu ‘yan bindiga suka harbe Olajide har lahira yayin da yake kan hanyarsa ta komawa Benin daga Legas inda yake karatu a Jami’ar Igbinedion.

“Mutuwar Olajide abin bakin ciki ne, za mu yi iya bakin kokarinmu wajen ganin mun hukunta wadanda suka shuka wannan ta’asa.” Gwamna Obaseki ya fada a shafinsa na Facebook.

“Ina mai mika sakon ta’aziyyata ga iyalan Sowore da kuma mawallafin Sahara Reporters Omoleye Sowore bisa wannan mutuwa ta dan uwansa Olajide Sowore.”

Hukumomin tsaro sun ce ‘yan bindigar da suka kashe Olajide sun sace wasu mutane biyar da suke tare da shi.

A gefe guda kuma, tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, shi ma ya yi Allah wadai da kisan Olajide.

“Na samu labarin kisan Mr Olajide Sowore, dalibi a jami’ar Igbinedion kuma kani ga mai fafutukar kare hakkin bil adama @YeleSowore.”

“Mutuwarsa, da kuma kashe-kashen da ake yi a kullum, na mutunen da ba su ji ba, ba su gani ba, na bakanta min rai.” Atiku ya fada a shafinsa na Twitter.

Matsalar garkuwa da mutane ta zama ruwan dare a Najeriya musamman a arewa maso yammacin kasar, inda ‘yan bindiga suka mayar da satar mutane tamkar sana'a.

Lamarin ya kai ga har suna sace dalibai da malamansu, abin da ya sa gwamnatocin jihohin yankin arewa maso yammaci da dama suka rufe makarantu har da ma kasuwanni.