Obasanjo Ya Soki Buhari Akan Yunkurin Ciwo Bashi daga Waje

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

A wata lakcar tunawa da Chief Akintola Williams tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya soki gwamnatin Muhammad Buhari da kakkausan lafazi domin yunkurin ciwo bashi daga waje na dalar Amurka biliyan talatin

Chief Obasanjo ya kuma soki gwamnatin Buhari dangane da matsalolin da kasar ke fama dasu a arewa maso gabashin kasar wurin yaki da ta'adancin Boko Haram na cewa sojojin Najeriya sun yi abubuwa na asha kuma na kunya.

Amma kuma a wani hannun Obasanjo ya jinjinawa gwamnatin akan yakin da ta keyi da cin hanci da rashawa musamman a bangaren alkalan shari'a. Ya kuma kira gwamnatin Buhari da ta duba wasu sassan musamman bangaren 'yan majalisa.

Ya kira gwamnatin Buharin da ta daina ratayawa gwamnatin baya duk matsalolin da kasar ke fuskanta yau. Yace dama sabili da matsalolin ne aka zabi gwamnatin domin ta kawo canji.

Ga rahoton Umar Faruk Musa da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Obasanjo Ya Soki Buhari Akan Yunkurin Ciwo Bashi daga Waje - 4' 19"