Obasanjo Ya Mika Kansa Kawai a Bincike Shi - Fayose

Tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo

A Najeriya, ana ci gaba da cece-ku-ce- kan kalaman da tsohon shugaban kasar, Olusegun Obasanjo ya yi, na cewa gwamnatin Shugaba Buhari na kokarin ta sa a kama shi.

Gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya kalubalanci tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo, da ya mika kansa domin a bincike shi, a maimakon ya rika shewar cewa gwamnatin Buhari na so ta kama shi.

A karshen makon da ya gabata, Olusegun Obasanjo, ya fitar da sanarwa ta hannun mai watsa labaransa, Kehinde Akinyemi, yana mai zargin cewa gwamnatin Buhari na yunkurin ta kama shi.

Sai dai a martanin da gwamna Fayose ya mayar kan kalaman na Obasanjo, wanda jaridar yanar gizon Premium Times ta wallafa a shafinta, ya ce, kada Obasanjo ya janyo kowa cikin matsalarsa.

Fayose ya kuma ce kada tsohon shugaban ya mayar da lamarin, batu da ya shafi kabilar Yarbawa, yana mai cewa maganinsa (shi Obasanjo) da ya marawa Buhari baya a shekarar 2015.

“Ni a nawa ganin, Obasanjo ya mika kansa kawai domin a bincike shi.” Inji gwamna Fayose.

Ya kara da cewa, shi Obasanjo “ya sha nuna mana cewa shi jarumi ne wanda ba ya tsoron komai, kuma Janar din soja ne da ya yi ritaya, saboda haka, ya daina kuwwar neman taimako.”

Zargin da Obasanjo ya yi, ya janyo hankula da dama a fagen siyasar Najeriya inda ake samun masu sukar shi da kuma masu mara mai baya.

Ita gwamnatin ta Buhari ta bakin ministan yada labaranta, Lai Mohammed, ta musanta wani yunkurin kama Obasanjon, tana mai cewa kalaman nasa, dabara ce ta dauke hankalin gwamnati wajen gudanar da ayyukanta.

Lai ya kara da cewa, da ma “mai kaza a aljihu ba ya jimirin as.”