Obasanjo Ya Baiwa Atiku Goyon Bayansa

Tsohon shugaban kasar Najeriya Olusegun Obasanjo.

Tsohon shugaban kasar Najeriya Olusegun Obasanjo ya bayyana goyon bayansa ga tsohon mataimakinsa dan takarar shugaban kasar Najeriya Atiku Abubakar.

A wata ganawa da suka yi da sauran mukarrabansa babbar jam’iyyar adawa ta PDP a garin Abeokuta, Obasanjo ya bayyana cewa a matsayinsa na Krista yafiya ga wanda yayi maka laifi abin yi ne, don haka ya yafewa Atiku game da laifukan da ya aikatawa ‘kasa da jam’iyya da kuma shi kansa.

Lokacin wannan ganawa da ta samu halartar shugabannin jam’iyya da na addinai irin su Mathew Hassan Kukah da Sheik Ahmad Gumi, Obasanjo ya ce Atiku zai fi shugaba mai ci yanzu tabuka abin azo a gani wajen jagorancin kasa.

Wasu daga cikin magoya bayan jam’iyyar PDP sun bayyana ganawar Atiku da Obasanjo a matsayin abin yabawa matuka wanda zai taimaka wajen samun nasarar jam’iyyar PDP a zabe mai zuwa.

Sai dai magoya bayan shugaba Muhammadu Buhari da jam’iyyar APC, na ganin ganawar Atiku da Obasanjo ba zai hana jam’iyya mai mulki samun nasara ba a zabe mai zuwa.

A baya Obasanjo ya sha bayyana Atikuk Abubakar a matsayin wanda yayi kaurin suna wajen cin hanci da rashawa, kuma ko a kwanan nan a wata cacar baka Obasanjo ya ce ba zai yafe masa ba.

Kafin wannan ganawa ta Obasanjo da Atiku sai da kungiyar Yarabawa ta Afenefere ta gana da Obasanjo, inda ta roke shi da ya yafewa Atiku kan laifin da yayi masa, a kokarin da yake na zama shugaban kasa.

Yanzu dai da yake Obasanjo yayi amai ya lashe akan Atiku, sai dai jiran ganin tasirin da goyon bayan zai haifarwa Atiku da jam’iyyar PDP a yankin Kudu maso Yammacin Najeriya da kuma sauran sassan kasar.

Domin karin bayani saurari rahotan Babangida Jibrin.

Your browser doesn’t support HTML5

Obasanjo Ya Baiwa Atiku Goyon Bayansa - 3'46"