Obama ya yi kira ga Sudan da Sudan ta Kudu game da batun zaman lafiya

  • Ibrahim Garba

Sudan na shagulgulan sake kwato Heglig

Shugaban Amurka Barack Obama ya shirya sako ta kafar ‘bidiyo’ ga Sudan

Shugaban Amurka Barack Obama ya shirya sako ta kafar ‘bidiyo’ ga Sudan da Sudan ta Kudu da aka yada a yau Asabar, inda ya ce “tashin hankali ba labudda ba ne,” kuma Shugabannin kasashen na da zabin kauce wa jefa kasashen cikin yaki.

A jawabin nasa ta kafar “You Tube” Obama ya yi kira ga kasashen biyu su kawo karshen daukar matakan soji kan juna. Y ace yakamata Shugabannin kasashen biyu su yi ta maza su koma kan teburin tattauna hanyoyin warware takaddamar cikin lumana.

Sakon na Shugaba Obama ya biyo bayan kwana da aka yi ana shagulgula a Sudan, inda ‘yan kasar da shugabannin jama’a su ka yi ta jinjina wa gwamnati, wadda ta yi ikirarin cewa dakarunta ne su ka kwato rijiyoyin man Heglig daga Sudan ta Kudu.

Shuagaban Sudan Omar al-Bashir ya jagoranci wani gangamin bayyana nasara a jiya Jumma’a a birnin Khartoun, a sa’linda da kuma sojoji cikin murna su ka yi ta shagulgula a Heglig da ake takaddama akai. Dalilan shagulgulan sun saba da bayanin Jakadiyar Sudan ta Kudu a MDD Agnes Oswaha.

Jakadiyar Sudan ta Kudun ta gaya wa manema labarai a hedikwatar Majalisar Dinkin Duniya da ke birnin New York a jiya Jumma’a cewa har yanzu dai dakarun Sudan ta Kudu ne ke da iko da illahirin Heglig. Ba ta tabbatar da da cewa da aka yi dukkannin dakarun Sudan ta Kudu za su bar Heglig cikin kwanaki 3 ba.

Sudan ta Kudu ta kwace Heglig mai arzikin mai ran 10 ga wata, wanda hakan ya janyo fargabar yaki gadan-gadan tsakanin kasashen biyu. A wani jawabin da ya yi ranar Laraba Shugaba Bashir na Sudan ya yi barazanar murkushe gwamnatin Sudan ta Kudu.

Ministan Yada Labaran Sudan ta Kudu ya fadi ranar Jumma’a cewa har yanzu Sudan ta Kudun na daukar Heglig a matsayin yankinta kuma ta na son Kotun Duniya ta fayyace makomar wurin da ma sauran wuraren da ake takaddama akansu.