NYSC: Aikin Bautawa Kasa Na Karfafa Cudanya da Fahimtar Juna

Shugaban Sashen Hausa na Muryar Amurka, Leo Keyen.

Aikin bautawa kasa a Najeriya da ake kira NYSC an kirkiroshi ne lokacin gwamnatin Janar Gowon shekaru uku bayan yakin basasan kasar saboda hada kawunan kabilun kasar domin tabbatar da zaman lafiya.

Shugaban Najeriya ya sha alwashin inganta shirin bautawa kasa da aka sani da NYSC.

Shugaban yace dalilan da ya sa aka kafa shirin suna nan kuma shirin ya taimaka wurin kawo cigaban al'ummomin Najeriya.

A nan Muryar Amurka shugaban sashen Hausa yace shi ya yi aikin bautawa kasa a shekarar 1979 a jihar Ogun cikin kabilar Yoruba. Kafin ya tafi yace shi bai san yarbawa ba.

A cewarsa yana ma tsoron cudanya dasu ko cin abincinsu. Amma yadda aka karbeshi a Ijebu Ode abun ya bashi mamaki. Bayan shekara daya bai so komawa jiharsa ta asali wato jihar Filato ba.

Shi ma Salihu daga Sokoto wanda yayi bautar kasa a shekrar 1974 ya je jihar Gabas ta Tsakiya ta lokacin wadda yanzu ta zamo jihohi biyar na kabilar Ibo. Kafin 1974 Salihu yace shi bai taba zuwa kasar Ibo ba.

Ya tuna suna yara ana ja masu kunne su guji kabilar wai domin suna cin mutane. Haka ma wasu 'yan ajinsa suka shiga yi masa jaje domin rashi kasar Ibo suna fata Allah ya sa ya dawo lafiya. Sai ya zamao abun tausayi domin ba'a dade da gama yakin basasa ba

Abun mamaki wani mutumin kauyen da ya zauna ya bashi wani bangaren gidansa a wani matsayi na nuna godiya. Mutumin yace lokacin yaki sojoji sun so su rushe gidan amma wani Kefen Sabo Sokoto ya hana.

Shi ma Ladan Ayawa yace saboda jin dadin zaman da yayi a Oyo inda ya bautawa kasa bayan shekara daya sai da ya kara biyu a kai yana aiki.

Ga wadannan mutanen bautawa kasa ya taimakesu fahimtar mutanen da aka ja kunnuwansu kada su yi kusa dasu.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

NYSC: Aikin Bautawa Kasa Na Karfafa Cudanya da Fahimtar Juna