Nwabali Ya Samu Gagarumar Tarba A Chippa United Sakamakon Bajintar Daya Nuna A Gasar AFCON

Nwabali

Kungiyar kwallon kafa ta Chippa United ta wallafa a shafinta na X cewar, Nwabali na daga cikin ‘yan wasan da suka yi fice a gasar cin kofin nahiyar Afirka (AFCON) na shekarar 2023.

‘Yan wasa da masu horas da kungiyar kwallon kafa ta Chippa United sun yiwa me tsaron ragar tawagar Super Eagles ta Najeriyya gagarumar tarba sakamakon bajintar daya nuna a gasar cin kofin nahiyar afrika (AFCON) da ta gabata.

Nwabali dan asalin Najeriya ya buga dukkanin wasannin da tawagar Super Eagles din ta fafata har zuwa karawar karshe ta gasar ta AFCON, inda suka yi rashin nasara a hannun masu masaukin baki kasar Ivory Coast.

Nwabali ya tare bugun fenariti har sau 2, abinda ya baiwa Najeriya damar samun nasara kan Afrika ta Kudu a wasan daf dana karshe, al’amarin daya kara masa farin jini.

Tun bayan kammala gasar, dan wasan yake ta samun yabo ta ko’ina. Don haka bayan komawarsa kungiyarsa a talatar data gabata, ‘yan wasa da masu horaswa suka shirya masa gagarumar tarba.

Mai tsaron ragar Super Eagles yayin da ya koma Kungiyar Kwallon Kafar Chippa United

Kungiyar kwallon kafar Chippa United ta wallafa cewar “ya dawo” a shafinta na X tare da hotunan yadda ‘yan wasanta da jami’ai ke tarbar tsohon dan wasan kungiyar Eyimba United ta birnin Aba.

Mai tsaron ragar Super Eagles yayin da ya koma Kungiyar Kwallon Kafar Chippa United a kasar Afirka ta Kudu