Yace tausayawa talakawa, aiki ma kasa da kawar da zalunci da talauci da suka kafu a Najeriya, sune suka sa jam'iyyunsu suka hadu suka kafa APC
WASHINGTON, DC —
Tsohon madugun yaki da zarmiya da cin hanci na Najeriya, kuma mutumin da yayi ma jam'iyyar ACN takara a zaben shugaban kasa na 2011, Nuhu Ribadu, ya bayyana farin cikin rajistar da hukumar zaben Najeriya ta yi ma sabuwar jam'iyyar nan ta APC.
A hirar da yayi da wakilin Sashen Hausa, Saleh Shehu Ashaka, Malam Nuhu Ribadu, ya bayyana sabuwar jam'iyyar APC a zaman hadaka ta al'ummomin kowane yanki na Najeriya, wadanda suka damu da halin da Najeriya ta shiga na zalumci da talauci da bakar wahala, da kuma rashin bin doka daga bangaren jam'iyya mai mulkin kasa da 'ya'yanta.
Yace wannan abu ne da bai taba faruwa a tarihin Najeriya ba, yadda manyan jam'iyyun hamayya suka yarda suka hade, domin yaki ma talakawan kasa. Yace hukumar zaben Najeriya ma ta taka rawar gani wajen yin rajistar, duk da yankan bayan da ake yi na tabbatar da cewa hakan bai faru ba.
Ga cikakken ba7yani daga bakin Nuhu Ribadeu nan...

Your browser doesn’t support HTML5