Tsohon shugaban hukumar dake yaki da cin hanci da rashawa kuma tsohon dan takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar ACN wadda yanzu ta narke cikin APC ya yi jawabi a Yola inda ya zargi PDP da neman wargaza Najeria.
Alhaji Nuhu Ribadu ya ce idan 'yan Najeriya basu tashi tsaye ba sun kawar da jam'yyar PDP daga mulkin Nigeriya to ko zata wargaza kasar. Ya ce jam'iyya ce mai danne hakin 'yan kasar tana aiwatar da mulkin kama karya. Gwamnatin kasar karkashin PDP bata yin adalci sai barna da kudin kasar da kare cin hanci da rashawa wadanda suka yiwa kasar katutu.
Shi ma yayin da yake jawabi tsohon minista a karkashin PDP Chief Fani Kayode cewa ya yi Najeriya a karkashin mulkin PDP ta zama kasa da bata da gaskiya sai dai mulkin kama karya da cin zarafin mutane. Ya ce PDP ta haddasa rashin tsaro a kasar tana cewa tana yaki da Boko Haram. Ya ce wa ya sani ko wasu manyan jam'iyyar suna cikin wadanda suke shirya Boko Haram suna daddasa rikicin da yaki ci yaki cinyewa. Idan babu hannun jigajigan PDP ciki yaya za'a ce gwamnati ta kasa murkushe kungiyar Boko Haram. Babu abun da ake yi sai hallaka rayukan mutane ta koina.
Da yake mayarda martani tsohon karamin minista a gwamnatin PDP Dr. Idi Hong kashedi ya yiwa 'yan Najeriya cewa kada su bari wadanda basu da matsayi su rudesu. Wadanda ke cikin APC yanzu daga wasu jam'iyyu suka fito inda basu samu sun cimma burinsu ba. Ya ce su da suka fita zasu dawo jam'iyyar PDP domin wasu da suka fita da can sun dawo.
Ga rahoto.
Your browser doesn’t support HTML5