NSA: Hukumar Leken Asiri Ta Naurori Ta Samu Sabuwar Doka

Shugaba Barack Obama na Amurka wanda tuni ya rabbataba hannu akan dokar.

Kamar majalisar wakilai ita ma majalisar dattawan Amurka ta amince da sabwar doka wadda hukumar leken asiri ta naurori zata yi aiki da ita.

Yanzu haka dai shugaba Barrack Obama ya sanya wa dokar nan data badadamar tattara bayanan kiran wayan salula da akayi a kasar wadda kuma zata hana yan ta’ada kaiwa kasar hari.

Mr Obama yace dokar zata kare kowa da kowa kana ta kara inganta matakan tsaro na kasa.

Tun farko dai yan majilisar dattijai sun jefa kuria kan wannan kudiri inda 67 suka rinjayi 32, dama dai majilisar wakilai ta amince da wannan kudirin.

Karkashin wannan sabuwar dokar kanfanonin sadarwa na tarho da hukumar leken asiri na kasa zasu tattara bayanan wayan tarho da Amurkawa suka yi, Kana masu bincike na kasa zasu bukaci umurni daga kotu domin su binciki bayanan da suka tattara daga wannan kiraye-kiraye musammam akan wadanda suke tuhuma suna da nasaba da ayyukan ta’addanci