Wani Ministan gwamnatin Sudan ya ce mai yiwuwa gwamnatin ta Sudan ta ki amincewa da sakamakon zaben raba gardama da ake shirin gudanarwa don sanin ko yan Kudancin na son su balle daga Arewacin Sudan ko a’a.
Ministan Matasa da Wasannin Motsa Jiki Haj Majid Suwar, wanda dan jam’iyyar su Shugaba Omar el-Bashir ce ta National Congress, ya zargi sojojin Kudancin Sudan da wuce iyakokin da aka shata masu a yarjajjeniyar zaman lafiya ta 2005.
Suwar ya gaya wa manema labarai cewa wajibi ne fa Kudancin Sudan su janye sojojinsu daga dukkannin wuraren da ake takaddama a kansu; su kuma bar masu sha’awar kasar Sudan ta cigaba da zama dunkulalliyar kasa suma su yi yakin neman zabe ba tare da wata tsangwama ba. In ko ba haka ba, in ji shi, Arewacin Sudan na iya watsi da sakamakon zaben ta kuma kai kara zuwa Majalisar Dinkin Duniya, da Amurka da kuma Kungiyar Hadin Kan Afirka.
Wani mai magana da yawun sojojin Kudancin Sudan ya gaya wa kanfanin dillancin labarai na Reuters cewa zargin bai da tushe. Ya ce dukkannin sojojinsu da cikin yankin Kudanci ne kuma sam ba su musguna ma kowane mai yakin neman zabe.
An shiga zaman dardar tsakanin Arewaci da Kudancin Sudan ganin an doshi zaben raba gardama game da yancin kai, wanda aka shirya za a yi ran 9 ga watan Janair.