NOMA TUSHEN ARZIKI: Yadda Annobar Cutar Korona Bairus Ta Shafi Harkokin Noma a Najeriya - Kashi Na Biyar, Disamba 29, 2020

Mohammed Baballe

Kamar yadda watakila wasu daga cikin masu sauraron mu suka ji a makon da ya gabata, muna tattaunawa ne kan yadda annobar cutar korona bairos ta shafi harkokin noma a Najerya da kuma barazanar yunwa da al’umar kasar ke fuskanta. Muna kuma tattaunawa ne da Farfesa Mohammed Faguji Ishiyaku, Babban darekta na cibiyar binciken harkokin noma ta Samaru da ke Zaria da kuma Dr. Shu’aibu Madugu, darekta a majalisar bincike harkokin noma ta Najeriya wato ARCN da ke Abuja.

A cikin shirinmu na wannan makon, wanda shine na karshe a wannan shekara ta 2020. Wakiliyarmu Medina Dauda ta tambayi, Farfesa Mohammed Faguji Ishiyaku, ko wane irin karbuwa wannan harkar kimiyya da fasa da suke kokarin fahimtar da monoma ta samu karbuwa.

Your browser doesn’t support HTML5

NOMA TUSHEN ARZIKI: Yadda Annobar Cutar Korona Bairus Ta Shafi Harkokin Noma a Najeriya - 6'00