WASHINGTON D.C. —
Yayin da ake cigaba da samun rikici tsakinin makiyaya da manona a wasu sassan Najeriya, gwamnatin jihar Neja da ke arewa ta tsakiyar kasar ta dauki mataki na warware wannan matsala da taki ci taki cinyewa, inda ta shuka wata ciyawa ta musamman a fili mai yawan kadada dubu 7 a babban gandun dajin nan na kamfanin Bobi da ke jihar.
A cikin shirin na mu na wannan makon, Mai Martaba Sarkin Muri, Alhaji Abbas Tafida, ya yi kari haske kan wannan ciyawa da aka siyo daga kasar Thailand da kuma hanyar da za'a bi don warware rikici tsakanin makiyaya da manoma.
Your browser doesn’t support HTML5