NNPC: Gwamnatin Najeriya Zata Raba Kamfanin Man Fetur Hudu

Karamin Ministan Man fetur na Najeriya Emmanuel Ibe Kachikwu wanda kuma shi ne shugaban kungiyar kasashen dake sayar da man fetur ta duniya ko OPEC.

Yayinda yake amsa tambaya gaban kwamitin dake kula da harkokin man fetur na Majalisar Dattawa Emmanuel Kachikwu ya sanarda shirin raba kamfanin NNPC hudu.

Gwamnati zata raba ma'aikatar man fetur din kashi hudu kuma kowane kamfani zai ci gashin kansa.

Kola Banwo na kungiyar dake sa ido akan harkokin tattalin arziki yana ganin zai haifar da da mai ido. Yace dama sun dade suna kukan a raba kamfanin NNPC domin an jibga mata ayyukan kamfanoni uku. Saboda haka rabawar ta dace domin cin hanci zai ragu.

Wani darakta a hukumar kula da hannayen jari a Najeriya Mansour Gwarzo yace bayan an raba NNPC to gwamnati ta dauki mataki akan kamfanonin hudu da za'a haifa. Misali yace kamfanin mai da na makamashi gwamnati ta matsa masu su koma hannun jari. Idan aka yi haka lamura zasu gyaru.

A wani bangare kuma kungiyar dillalen man fetur ta kasa tayi amanna da matakin da gwamnati ta dauka domin a cewar Abubakar Maigandi Dakingari, mataimakin kungiyar na kasa yace matakin zai taimakawa tattalin arzikin kasa. Yace da an tara ma'aikatan NNPC wuri daya kuma babu abun da suke kawowa gwamnati sai hasara mai dimbin yawa. Rabasu zai bada daman a san wanda ya yi kuskure ko ya aikata wani abu ba daidai ba.

Ma'aikatar ko NNPC zata samu kamfanin hako man fetur da kamfanin fitar da man, da kamfanin iskar gasa da kuma kamfanin gudanarwa.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

NNPC: Gwamnatin Najeriya Zata Raba Kamfanin Man Fetur Hudu - 2' 15"